Skip to main content.

 

Adedibu Ya Ce: Gwamna Abdullahi Adamu Zai Iya Kai Nijeriya Ga Tudun Mun Tsira


 UBAN siyasar Ibadan Alhaji Lamidi Adedibu ya ce ya gamsu cewa fafutikar da Gwamna Abdullahi Adamu na Jihar Nasarawa yake yi na neman shugabancin }asar nan a }ar}ashin jam’iyyar PDP, yana yi ne saboda zimmarsa ta neman kai }asar nan ga tudun mun tsira.

Alhaji Adebibu ya ce gadojin ha]in kai da kyakkyawar dangantaka da Gwamna Abdullahi Adamu ya gina a tsakanin ‘yan Nijeriya a shekara -da- shekaru a yanzu za su kasance masa matakala na kaiwa ga kujerar shugabancin }asar nan.

Cif Adedibu ya bayyana haka ne, lokacin da Gwamna Adamu ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke garin Ibadan.

Alhaji Adebibu ya bayyana Gwamna Adamu a matsayin "]alibi mai biyayya" ga shugaba Olusegun Obasanjo inda ya ce, irin wannan biyayya da gwamnan ya nuna ya jawo masa }auna da girmamawa daga magoya bayan wannan gwamnati. Ya ce, Gwamna Adamu ya mallaki basira da }arfin himmar da zai ciyar da Nijeriya gaba kamar yadda shugaba Obasanjo ya aza harsashin haka.

Sai ya ce, "Ina ro}on Allah cikin rahamarSa Ya sanya ka cikin mutanen da Zai ba su amanar ri}on }asar nan a shekara ta 2007, wannan ita ce addu’armu gare ka. Kuma a namu ~angare a shirye muke mu bayar da tamu gudunmawar."

Shi ma da yake magana kan takarar Gwamna Adamu tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Oyo Dokta Omololu Olunloye ya ce "Gwamna Adamu ]an takarar shugaban }asa ne da ya cancanta, wanda kuma na san shi fiye da shekara 30. Shi }wararre ne kuma fitaccen ]an siyasar da ya dace ya shugabanci tarayyar Nijeriya."

Dokta Olunloye ya yi al}awarin nema wa gwamnan goyon baya a yankin Kudu maso Yamma, ta hanyar bayyana musu kyawawan halayensa da nasarorin da ya samu.

Gwamnan ya kai ziyarar gidan gwamnati da ke Badun a inda ya sadu da gwamnan Jihar Oyo, Cif Bayo Alao Akala don bayyana bu}atarsa ga al’ummar Kudu maso Yammacin }asar nan, na neman su za~e shi.

Dokta Abdullahi Adamu ya ce, yana so ya shugabanci }asar nan ne don }arfafa ha]in kai da kawo ci gaba cikin hanzari.

Ya jaddada cewa, Nijeriya ta da]e tana fama da koma baya, amma sake haye mulki da shugaba Olusegun Obasanjo ya yi a shekarar 1999, an samu ci gaba mai ma’ana.

Gwamna Bayo Akala ya tabbatar wa gwamna cewa, al’ummar Jihar Oyo da kuma Yarbawa sun gamsu da yun}urinsa na neman shugaban }asa a matsayinsa na ginshi}in ha]a kai, tare da bayyana cewa, zai za~e shi don haye kujerar shugabancin }asar nan.

Gwmanan Abdullahi Adamu har ila yau, ya kai ziyarar ban girma ga fadar Olubadan na Ibadan da Alafin na Oyo, a inda ya bu}aci sanya albarkarsu, don cimma burinsa na kasancewa shugaban }asar nan.

Sarakunan gargajiyar guda biyu, sun yaba wa gwamnan saboda biyayya da kuma goyon bayansa ga shugaba Obasanjo, inda suka tabbatar masa da goyon bayansu.

A fadar Ooni na Ife, babban basaraken }asar Yarbawan Oba Okunade Sijuwade Olubuse II, wanda ya yi magana ta bakin jami’in hul]a da jama’arsa Funmilayo Olorunshola, ya ce Gwamna Adamu mutum ne abin dogaro a kowane lokaci, don haka ba ya da shakka kan zai iya bun}asa }asar nan idan ‘yan Nijeriya suka za~e shi a matsayin shugaban }asa.

Ooni na Ife ya ce, a matsayinsa na mai ri}e da sarautar Aare Obateru na }asar Ife, Gwamna Adamu ya zama ]a ga al’ummar Ife kuma wani }usa a fadar masarautar Ife.

Da yake mayar da jawabi Gwamna Adamu ya ce, ya je Ife ne don halartar bikin al’adu na shekara- shekara na Ife, kuma ya ce, Ooni na Ife yana ba shi shawarwarin da suke ]ora shi bisa gwadaben kirki a kodayaushe.

Ya kuma ce baya ga halartar bikin ya je birnin mai tsohon tarihi ne don shaida wa basaraken }udurinsa na neman shugabancin }asar nan tare da neman sanya albarka da yin addu’a daga sarkin.


Tuesday, November 28, 2006