Shugaban Majalisar Dokokin Kano Ba Zai Sake Tsayawa Takara Ba
Daga Ibrahim Garba, Kano
SHUGABAN majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Balarabe Sa’idu Gani, ya ce a kai batun tsayawarsa takara a za~en 2007 kasuwa domin ba zai sake tsayawa takara a yanzu ba.
Wannan matsayi na shugaban majalisar ba zai rasa nasaba da irin yadda wa]ansu jama’a ke }o}arin kawo masa tawaya a maza~arsa ta }aramar hukumar Sumaila ba.
Shugaban majalisar wanda ya sha tsallake yun}urin tsigewa daga masu adawa da tafiyarsa a majalisar dokokin ta Kano ya ce halin da ake ciki yanzu ba shi da wani buri na sake tsayawa takara a za~e mai zuwa.
AlhajiBalarabe Gani ya kuma bayyana cewar tsawon shekara hu]u da ya gudanar akan wannan mu}ami abin alfahari ne gare shi da ya cancanci samun yabo daga dukkan Kanawa, domin ya taimaka wajen kawo sauyi na harkokin rayuwar jama’ar Kano.
Shugaban majalisar dokokin wanda ya shaida wa ‘yan jarida hakan a }arshen makon jiya, ya kuma ce kamata ya yi dukkan mai mulkin da ya yi sau ]aya ya ha}ura don bai wa sababbin jini damar bayar da tasu irin gudunmawar.
Ya kuma bayyana cewar zai ci gaba da bai wa dukkan mai son kawo ci gaba a Kano ha]in kai don bun}asar rayuwar jama’a.
Alhaji Balarabe ya kirayi jama’a da su sabunta rijistarsu don ita ce ka]ai hanyar kawo sauyi mai ma’ana a tsarin mulki irin na dimokura]iyya a }asar nan.
Tuesday, November 28, 2006