Fulani Makiyaya 6,000 Suka Yi Hijira Daga Zamfara
Daga Sanusi Mohammed, Gusau
KIMANIN fulani dubu shida ne aka gano sun yi hijira daga Jihar Zamfara zuwa jihohin Katsina da Kebbi da Kaduna da Neja da kuma Kano a shekara biyu da suka gabata a sakamakon sayar da dazuzzukan da suke kiwo da gwamnatin jihar take yi ga manoman jihar.
Fulanin kamar yadda Nasara ta gano sun fito ne daga ~angaren Zurmi da Shinkafi da Mafara da [ansadau da Kanoma da Gumi da Anka da Bakura da ke jihar ta Zamfara.
Su dai fulanin wakilinmu ya gano mafi yawansu an haife su ne a guraren da suke tashi, kuma sun yi duk }o}arinsu wajen ganin gwamnatin jihar ta bar musu dazuzzukan amma ta yi kunnen uwar shegu da su kimanin shekara biyu da suka gabata.
Da yake zantawa da Nasara wani Bafillace mai suna Alhaji Malicci ya ce ya gina gida a dajin [ansadau kuma ya kashe fiye da Naira dubu 700 wajen gina gidan kuma ya shekara ta fi 40 amma ga shi an sayar da sashinsa da }arfin tuwo.
Kan haka ne }ungiyar Miyetti Allah ta shirya wani taro a garin Kanoma da ke }aramar hukumar Maru don lalubo hanyoyin da za su bi wajen magance wannan matsalar.
A jawabinsa shugaban na Miyetti Allah, Alhaji Bello Liman Anka ya ce za su bi duk hanyoyin da suka dace wajen tuntu~ar gwamnatin jihar don magance matsalar.
Alhaji Bello Liman, wanda ya bayyana fulanin jihar a matsayin masu biyayya ga shirye-shiryen gwamnatin jihar, daga nan ya yi kira ga sauran fulanin da suka rage da su zauna lafiya tare da ci gaba da biyayya ga gwamnati don sun }uduri aniyar shawo kan matsalar cikin sau}i.
Daga nan ya yi kira ga gwamnatin Jihar Zamfara da ta dubi Allah ta tausaya wa al’ummar fulanin jihar.
A wata mai kama da hakan Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Ahmed Sani ya kafa kwamitin gaggawa mai ]auke da mutum 23 }ar}ashin jagorancin Alhaji Ahmed Abdul-Nasir babban sakataren mai kula da harkokin gwamnatin jihar domin duba matasalar da fulanin suke ciki tare da ziyartar duk inda ake da matsala don nemo maslaha.
Tuesday, November 28, 2006