Sanata Isa Mohammed Ya Muzanta Janar Buhari
SANATA Isa Mohammed na jam’iyyar PDP daga Jihar Neja, ya muzanta tsohon shugaban }asa Janar Muhammadu Buhari, inda ya yi }o}arin hana shi yin magana wajen }addamar da wani littafi kan shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani saboda abin da ya kira Buharin ya ta~a kawar da gwamnatin dimokura]iyya a Nijeriya.
Al’amarin wanda ya auku a ranar Larabar da ta shige aAbuja, ya auku ne ne lokacin da Janar Buhari ya taso daga rumfar manyan ba}i don yin jawabi a taron, amma sai Sanata Isa Mohammed ya ce alambaran Buhari ba zai yi magana ba, domin a ganinsa Buhari ba ya da abin da zai iya cewa kan dimokura]iyya, saboda ya ta~a rusa gwamnatin dimokuradiyyar.
Ya nuna Buhari, ya ce, " wannan mutum ya rusa dimokura]iyya a }asar nan tare da cin fuskar sanatoci."
Ya }ara da cewa, "Janar Buhari ka wula}anta sanatocin tarayyar Nijeriya. Idan sauran sanatoci za su iya ha}uri da haka, ni ba zan iya ba. Kuma ina tabbatar maka tunda ka rushe gwamnatin dimokura]iyya a }asar nan, har abadan ba za ka ta~a zama shugaban }asa ba kuma".
Sanata Isa, wanda ‘yan uwansa sanatoci suka yi ta ro}on ya dakatar da cin zarafin Janar ]in ya ci gaba da cewa, "Janar Buhari ya sani fa ba zai ta~a sake mulkar }asar nan ba." Wannan kalami nasa ya harzu}a sanatoci da dama, har ta kai lokacin da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ibrahim Mantu yake jawabin godiya, ya tsame sauran sanatocin daga kalaman Sanata Isa Mohammed ]in.
Sanata Mantu ya ce, maganganun da Sanata Isa Mohammed ya yi ra’ayin kansa ne kawai, ba ruwan majalisar dattawa da su.
Ya nemi jama’a da su ri}a girmama na gaba, sannan ya nuna jin da]insa kan halartar bikin da mataimakin shugaban }asa Atiku Abubakar ya yi, a daidai lokacin da ake samun rahotannin da ke nuna cewa ya fice daga gidansa na gwamnati saboda dalilan tsaro. Sai dai Atiku bai yi jawabi wajen bikin ba.
Da yake jawabi wajen bikin Janar Muhammadu Buhari ya yaba wa kyakkyawan shugabancin shugaban majalisar dattawar, musamman yadda ya tafiyar da batun ta-zarce karo na uku. Sai dai kuma ya }alubalanci shugaban majalisar da ya binciki zargin bayar da cin hanci ga ‘yan majalisar a daidai lokacin da ake muhawarar.
Janar Buhari, ya ce ya yi magana da Sanata Ken Nnamani kan ya kafa wani kwamitin bincike da zai banka]o gaskiyar zargin bayar da hancin Naira miliyan hamsin-hamsin ga ‘yan majalisar a daidai lokacin da muhawara ta yi zafi kan batun, inda ya ce, yana fata za a kefa kwamitin tare da sanar da duniya sakamakon bincikensa.
Sauran wa]anda suka yi jawabi wajen bikin sun ha]a da Cif Sunday Awoniyi, shugaban }ungiyar kare muradun Arewa (ACF) da shugaban }asa Cif Olusegun Obasanjo da shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani, yayin da Fada Mathew Hassan Kukah ya yi nazarin littafin.
Tuesday, November 28, 2006