Skip to main content.

 

Ina Nadamar Barin Amurka Ta Mamayi Ira}i - Kofi Annan


BABBAN sakataren majalisar ]inkin duniya mai barin gado, Mista Kofi Annan ya ce yana nadamar barin Amurka ta mamayi Ira}i, a daidai lokaci da ya ce, Ira}i ta kasance wa Amurka ‘}adangaren bakin tulu’ inda ya nemi gwamnatin Amurkan ta bi a sannu kan shirinta na ficewa daga Ira}in ta yadda ficewar tata ba za ta }ara jefa }asar a cikin mummunar matsala ba.

Mista Annan ya fa]i a birnin Geneva a makon da ya wuce cewa akwai bu}atar gwamnatin Amurka ta tabbatar "ficewar ta daga Ira}i bai da]a sukurkuta harkar tsaro a }asar ta Ira}i ba."

Mista Annan ya ce, "ga dukkan alamu Amurka tana fuskantar wani yanayi na gaba kura baya siyaki a }asar Ira}i, ta yadda ba za ta iya ci gaba da kasancewa a }asar ba, sannan fita daga cikinta ya gagare ta." Ya ce, akwai masu ganin ci gaba da kasancewarta a Ira}i matsala ce, sannan kuma idan ta fice to, al’amura za su da]a jagwalgwalewa."

Mista Annan wanda wa’adinsa a kujerar zai }are ranar 1 ga Janairu 2007, ya ce ya}in da ya auku a Ira}i da gazawar kwamitin sulhu na majalisar ]inkin duniya, ya hana Amurka mamayar }asar Ira}i shi ne babban abin da ya fi nadama a kai a shekara 10 da ya yi kan kujerar magatakadar majalisar ]inkin duniya.

Ya ce, "na ha}}a}e ana iya kauce wa ya}in kuma sufetocin majalisar ]inkin duniya suna iya ci gaba da binciken makaman da suke yi har su gano gaskiyar al’amura.


Tuesday, November 28, 2006