Skip to main content.

 

An Ba Hammata Iska Tsakanin Magoya Bayan ‘Yan Takarar Gwamna Na PDP A Gombe


Daga Abubakar Rabilu, Gombe

YUN{URIN ]an majalisar dattawa mai wakiltar maza~ar Gombe ta Tsakiya, Injiniya Sa’ad Mohammad Abubakar na tsayawa takarar gwamna a jamm’iyyar su ta PDP, na neman zama masa ala}a}ai, domin akan hanyarsa ta shigowa garin Gombe, magoya bayansa da suka yi dafifi a wani }auye da ake kira Wuro-Dole da ke iyakar Bauci da Gombe domin maraba da shi, sun yi fito na fito da wa]ansu ‘yan adawa na cikin gida na ~angaren wani ]an takara.

A ranar Litinin ]in da ta gabata ne Sanata Sa’ad Mohammad ya je sakatariyar jam’iyyarsu ta PDP domin yankan takardarsa ta tsayawa takarar kujerar gwamna a Jihar Gombe, inda dubban magoya bayansa suka yi cincirindo domin nuna farin cikinsu da goyon bayansu gare shi, domin a cewar su, shi ne ]ansu da zai }wato musu ‘yancinsu da suka rasa a baya.

Bayan Injiniya Sa’ad ya kar~i takardar ta tsayawa takara a sakatariyar jam’iyyar ta PDP da ke kan hanyar zuwa Biu, sai tawagarsa ta zarce zuwa mahaifarsa ta garin Deba wanda a can ne aka shirya masa liyafa ta musamman domin murna.

Da isar tawagar Injiniya Sa’ad garin Deba, sai ya wuce zuwa maza~arsa domin sabunta katin za~ensa, wanda kafin wucewar tawagar zuwa fadar Mai martaba Sarkin Deba. Alhaji Abubakar Mahdi, Injiniya Sa’ad ya yi hira da ‘yan jarida inda ya shaida musu }udurinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar.

Injiniya Sa’ad ya bayyana godiya ga magoya bayansa kan irin ha]in kan da suke ba shi inda ya ce idan ba da goyon bayansu ba, ba zai sami ]arewa a bisa karagar mulki ba don haka yake mai sake ro}onsu da su daure, kar su gajiya har sai an yi za~e sun ga sun sami nasara.

Har ila yau ya kuma bayyana cewa kowa yana da damar za~en wanda ya kwanta masa a rai a kuma kowace jam’iyya yake hakan kuma ba shi ne zai sa mutum ya zama ]an ta’adda ba.

Sa’anan kuma ya sake bayyana jam’iyyarsu ta PDP da cewa jam’iyya ce mai farin jini kuma wacce ba ta }yamar kowa, don haka ya ga ya dace ya dawo takara a cikin ta a matsayin gwamna ba na sanata ba.

Daga bisani Injiniya Sa’ad, ya ci gaba da cewa shi bai nemi tsayawa takara domin haddasa fitina a tsakanin al’umma ba, don haka, mene ne ya sa wa]ansu tsirarru za su nemi tayar wa magoya bayansa hankali, inda ya bayyana cewa a tsiraru shi an farfasa masa motoci guda 29 kuma an yi wa wa]ansu daga cikin magoya bayansa miyagun raunuka.

Wani na hannun damar sanatan wanda kuma tsohon kwamishina ne da ya bar aiki a wannan gwamnati mai ci, Laftana Kanar Magaji Kuji Filam, ya }alubalanci gwamnatin Jihar kan rashin kyakkyawan tsaro a tsakanin al’umma, wanda a cewarsa ya kai, idan kai ba ka iya ta’addanci ba, kai ba komai ba ne, "domin za a dinga yi wa rayuwarka barazana, a kullum za ka kasance kana cikin ]ar-]ar ba kwanciyar hankali" inji shi.

 


Tuesday, November 28, 2006