‘Yan Jarida Sun Yi Barazanar Janyewa Daga Yayata Harkokin Siyasa A Barno
{UNGIYAR ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ) a Jihar Barno ta yi barazanar cewa, wakilanta, za su janye daga yayata harkokin siyasa a jihar.
Shugaban }ungiyar ‘NUJ’ a jihar, Mala Baba Kura Bukar ne ya bayyana haka a inda ya ce, tilas ne masu takarar siyasa a jihar, su yi wa magoya bayansu garga]i, tare da samar da kyakkyawan yanayi na gudanar da aiki ga ‘yan jarida a jihar.
Rahotanni sun ce, ‘yan jaridar sun yi wannan barazanar ce, bayan da wa]ansu ‘yan jarida da suke ]aukar rahotanni a game da ziyarar da ]aya daga cikin ‘yan takara shugabancin }asar nan }ar}ashin PDP ke yi a jihar, wa]anda ‘yan bangar siyasa suka musguna masu a Maiduguri babban birnin jihar.
Tuesday, November 28, 2006