Skip to main content.

 

Jam’iyyar PDP Ta Fitar Da Sakamakon Za~en Fitar Da Gwani A Jihar Nasarawa


Daga Musa Isa, Lafiya

JAMI’IYYAR PDP a Jihar Nasarawa ta fitar da sakamakon za~en fitar da gwani da aka yi a ranar Asabar waccan da ta shige a jihar.

Shugaban PDP a jihar, Alhaji Yusuf Ayitogo (Katukan Adudu) wanda ya bayyana sakamakon za~en ya bayyana za~en da cewa an gudanar da shi babu cuta kuma an gudanar da shi cikin ri}on amana a cikin tarihin jihar.

Alhaji Yusuf Ayitogoya ya c, za~en fitar da gwani da aka yi, an kammala cikin nsara da kuma kwanciyar hankali a ko’ina a jihar.

Alhaji Yusuf Ayitogo ya yaba wa wakilai jam’iyyar saboda halin ya kamata da suka nuna inda ya yi kira a }ara samun fahimtar juna a tsakanin ‘yan siyasa da ke jihar.

Sakamakon da ya bayyana ga manema labarai ya nuna cewa, a maza~ar Doma ta Arewa, Mohammad Ogoshi Onawo ne ya lashe za~en, a Akwanga ta kudu kuwa, Philip Aruwa Gyunka ne sa’anan a Eggon ta Gabas, [anlami Mohammad Idris ya lashe za~en, a Lafiya ta Tsakiya kuwa Adamu Liman ne. A maza~ar Keana Yakubu Dodo ne ya lashe za~en.

A maza~ar Wamba Yukubu Abdulhamid Kwarra ne, a Keffi ta Gabas, Bamamasi [ahiru, Akwanga ta Arewa Mbucho Peter, Keffi ta Yamma, Abdullahi Musa Aliyu, Awe ta Arewa, Yakubu Faransa, Kokona ta Gabas, Raphael Dogora Saska, Lafiya ta Arewa, Adamu Mu’azu.

Haka nan kuma a Obi ta biyu, akwai Elisha Agwadu, Kokona ta yamma, Ishaq Ahmed Kana, Obi ta ]aya, Alhaji Sidi Mohammad Ba}o, Nasrawa ta Tsakiya, Musa Ahmed Mohammad Sai Uke Karshi, Tahir Alayi.

Sauran sune Doma ta Kudu, Ahmed Sardauna Eyibo, Loko/Udege Patrick Ebinny, Gadabuke/Toto Adams Gwamna Nyisana, Karu/ Gitata, Bala Elang, Ugya/Umaisha, Yahaya Ohinoyi Usman, Eggon ta Yamma, Samuel Allu sai Awe ta Kudu Jada Hashimu.

Shugaban ya ce, an kafa kwamitin da zai amince da sakamakon za~en da aka yi a Awe ta Kudu, sakamakon bayanin da aka samu daga jami’in bada sakamakon da kuma tabbacin da aka samu daga shugaban jam’iyyar a yankin raya }asa na Azara.

 


Tuesday, November 28, 2006