{aramar Hukumar Keana Ta Yi Al}awarin Bayar Talafi Ga |angaren Ilimi.
MAHUKUMTA a }aramar hukumar Keana da ke Jihar Nasarawa sun yi al}awarin ci gaba da bayar goyon baya, don bun}asa ilimi a yankin.
Shugaban }aramar hukumar, Dokta Ahmed Alaga ne ya bayyana haka a wani kwas na sanin makamar aiki na kwana ]aya da aka shirya a yankin inda ya ce, don tabbatar da bun}asar ilimi, ya zama tilas a rin}a }ara wa malamai ilimi ta hanyar shirya masu kwas na sanin makamar aiki.
Shugaban }aramar hukumar ya ce, daga cikin yun}urin da ya yi na bun}asa ilimi a yankin, gwamnatinsa ta sayo kujeru da tebura, da bayar guraben }aro ilimi ga ]aliban makarantun sakandare da na gaba da sakandare kazalika kuma da ]aukar malamai aiki da dai sauran su.
Da yake jawabi a wajen taron bitar, wakilin kwamishinan ilimi na jihar, lliya Buku ya yaba wa shugaban, saboda shirya wannan kwas na sanin makamar aiki, tare da kiran sauran shugabannin }ananan hukumomi jihar kan su yi koyi da shi.
Daga cikin muhimman abubuwan da aka yi a wajen taron, sun ha]a da aza harsashin ginin azuzuwa uku, da }aramar hukumar ta gina wa makarantar kurame da ke hedkwatar }aramar hukumar.
Tuesday, November 28, 2006