Wani Abu Kan Tsarki
Ruwa mai tsarki
RUWAN sama da na teku da na kogi da na rijiya, ruwa ne mai tsarki. Abin da a ke kira ruwa mai tsarki, shi ne wanda ]ayan siffofinsa uku ba su sake ba. su ne launinsa, ko sha}ensa, ko ]an]anusa.
Irin wannan ruwa shi ne mai tsarki a kansa, kuma mai tsarkakewa. Da irinsa a ke yi alwalla, ko wanka na ibada. Kamar wankan janaba, da haila, da na zuwa jamma’a ko na ranar Idi, da na tsayuwar Arafa. Da irinsa ne kuma a ke wanke najasa wadda ta taba jikin mutum ko tufafinsa.
Ruwan da ya sake
Ruwan da ]ayan siffofinsa ya sake da abu mai tsarki, kamar madara, ko zuma, ko gari, shi ruwa ne mai tsarki a kansa ka]ai, amma ba mai tsarkakewa ba. Sabo da haka ana iya yin amfani da shi a wajen al’ada kawai. Kamar sha, ko dafuwar abinci, ko wanke-wanke. Amma ba za a yi amfani da shi a wajen ibada ba, kamar alawalla.
To, amma ruwan da ya sake da najasa, kamar ta fitsari, ko kashi, ko jini, to, ba shi da tsarki shi kansa, kuma ba ya tsarkakewa. Sabo da haka ta za a yi amfani da shi ba, ta wajen al’ada ko ibada.
Amma idan ruwa ya sake da wani abu wanda ya ke mazauninsa ]aya da ruwa tun asali, kamar idan ya sake da }asa ko wace iri, ko gishiri, ko kanwa, ko gansa kuka, ko don tsawon ajiyewa, to, wannan sakewar ba za ta shafi tsarkinsa ba. Watau ana iya amfani da shi ta wajen al’ada ko ibada.
Tsarki ga mai salla
Wajibi ne ga dukkan wanda zai yi salla, ya zama jikinsa da tufafinsa da wurin da zai yi salla, duk suna da tsarki. Amma da shara]in ya tuna da samuwar najasar, kuma ya zama yana da ikon gusad da ita. Sabo da haka, idan mutum ya manta ya yi salla da rufa mai najasa, ko a kan wuri mai najasa, bai tuna ba sai bayan ya rigaya ya yi sallama, to, sallarsa ta yi kyau. Sai dai mustahabbi ne gare shi ya sake sallar bayan ya manke najasar, idan lokacinta bai fita ba.
Misali na rashin iko kuwa, shi ne kamar idan mutum yana da najasa ga jikinsa ko tufafinsa, amma kafin ya sami ruwan wanke ta, lokacin yin salla zai fita, to, sai ya yi sallarsa hakanan da najasar. Ta kuwa yi kyau.
Dabba mai rai
Dukan abu mai rai - mutum ne ko dabba, tsauntsu ko }waro, to, zuffansa da yawunsa, da majinarsa, da hawayensa, da }wansa (idan ba dunge ba ne) duk tsarki gare su.
Nono
Nonon ‘yan Adam tsarki gare shi. Amma hukuncin nonon sauran dabbobi ya danganta ga yadda hukuncin cin namansu ya ke. Sabo da haka, idan dabba cinta halal ne, kamar saniya, da ra}uma, da tunkiya, da akuya, to, nononta tsarki gare shi. Idan kuwa cinta haramun ne kamar jaka, go]iya da alade, to, nononta najasa ne. Idan kuwa cinta makruhi ne, to, nononta makruhi ne. Kamar kyanwa da kura da zakanya.
Najasa
Kashi da fitsari na dabba wadda aka halatta cinta, tsarki gare su sai fa idan dabbar tana cin najasa, to, kashinta da fitsarinta najasa ne. Haka kuma dabbar da aka haramta cinta, ko aka karhanta cinta, to, kashinta da fitsarinta najasa ne.
Kama Ruwa
Fitsari da kashi na ]an Adam, ban da na Annbawa, najasa ne.
Idan dabba ta muru, mushe, to, duk jikinta ya zama najasa. Sai fa gawar mutum don darajarsa. Da kuma dabbar ruwa don ba ta bukatar yanka. Da kuma dabbar da babu jini gare ta tun halitta, kamar fara, }uda, tururuwa, tsutsa, kwarkwara, }u]in ciso da kaska.
Dukan abin da aka ]ebo daga jikir dabba mai rai, idan akwai rai ga ainihin abin, wasu dabbar za ta ji zafi a lokacin ]ibarsa, kamar }abo, }ashi, akaifa da fata, to, najasa ne.
Idan kuwa an yanka daba wadda ya haiatta a ci, to, kome na jikinta tsarki gare shi.
Ruwan }urji, da jini mai gudansa, da amai wanda ya sake daga halin abinci, da dubkan abu mai sa maye, najasa ne. Amma an yi rangwame ga jini wanda ya kasa dirhamul bagaliyyi, watau ]an tabon nan na jikin }afar gaba ta alfadari.
Maniyyi da maziyyi da wadiyyi, najasa ne.
Siffar maniyyin namiji ruwa ne fari, mai kauri, mai tunku]ar juna a wurin fitowarsa. Yana fitowa sabo da babbar sha’awa, kamar jima’i. Amma maniyyin mace shi ruwa ne tsanwa-tsanwa (rawaya), tsararo. Ana yin wanka domin fitowarsa.
Siffar maziyyi ruwa ne, fari, tsararo. Ya kan fito wurin }aramar sha’awa, kamar tashin zakari, ko wasa da mace, ko yi mata mugun kallo na sha’awa, ko tsananin tunaninta a cikin zuciya. Ana wanke dukan zakari domin fitowarsa.
Siffar wadiyyi ruwa ne, fari, mai kauri. Galibi ya kan fito a }arshen fitsari. Hukucinsa kamar na fitsari. Watau a wanke wurin da ya ta~a kawai.
Tokar }onanniyar najasa tsarki gar e ta a bisa }auli mashahuri.
Fasalin kama ruwa
Wanke kafar zakari da dubura bayan yin fitsari ko kashi, shi ne kama ruwa. Amma kafin mutum ya kama ruwa, ya wajaba gare shi ya yi istibra’i tukuna.
Istibra’i shi ne mutum ya sa zakarinsa tsakanin babban yatsansa da manuninsa na hannun hagu, sa’an nan ya mammatso ]an ragowar fitsarin nan da ya ma}ale a cikin kusuwar zakarinsa, sa’an nan ya kakka~e kan zakarinsa. Zai yi haka a hankali a hankali, har sau uku.
Bayan }are istibra’i, idan mutum ya goge zakarinsa da duburarsa da kyau, to, ba dole ne ya yi tsarki kuma da ruwa ba. sai dai am fi son yin amfani da ruwa. Guga ba za ta wadatar ba ga fitsarin mace, da kuma kashi ko fitsarin da ya watsu ya shige mahallinsa.
Ba a yin guga da abu mai santsi, ko mai kaushi ainun. Haka kuma ba a yi da dukan abu mai suman Ubangiji rubuce a jikinsa.
Idan mutum bai yi guga ba, ko kuwa ya yi, amma yana son ya yi amfani da ruwa, don am fi son hakanan, to, tun farko sai ya fara da wanke hannunsa na hagu. Sa’an nan ya wanke zakarinsa. Bayan ya }are kama ruwan, sai kuma ya wanke hannunsa da sabulu, ko kuwa ya goge shi da }asa, kana ya wanke.
Daga Littafin Ibada Da Hukunci Na Marigayi Sheikh Halliru Binji
An |u}aci Iyaye Da Su Yi Wa ‘Ya’yansu Allurar Rigakafin Shan Inna
AN yi kira ga iyayen yara a }aramar hukumar Doma da ke Jihar Nasarawa da su yi amfani da damar da hukumar shirin allurar rigakafi ta }asa ta bayar, don fito da ‘ya’yansu a yi masu allurar rigakafin cutar shan inna da ba}on dauro da sauran cututtuka masu kisan yara.
Shugaban kwamitin wayar da kan jama’a akan shirin allurar rigakafi a }aramar hukumar Doma, Hajiya A’ishatu Abdullahi ce, ta yi wannan kiran a makon jiya inda ta ce, samun nasarar shirin allurar rigakafi ga }anana yara akan cututtuka masu ya]uwa ya dogara ne a wuyan iyaye.
Hajiya A’ishatu Abdullahi wacce darakta ce mai kula da shirin kiwon lafiya a yankunan karkara ta }aramar hukumar Doma, ta tabbatar wa iyaye samun }oshin lafiyar ‘ya’yansu ta hanyar fito da ‘ya’yansu, don rigakafin cututtuka akai akai.
Zan Yi Aiki Tu}uru Don Bun}asa Jihar Nasarawa - Aliyu Doma
Labari Daga Musa Isa Lafiya
ALHAJI Aliyu Akwe Doma ]an takarar gwamnan Jihar Nasarawa a shekara ta 2007, }ar}ashin jam’iyyar PDP ya sake jadadda }udirinsa na yi wa al’ummar jihar aiki tu}uru, idan suka za~e shi a matsaying gwamnan jihar.
[an takarar wanda ya yi wannan tayin, ga al’ummar jihar a yayin }addamar da kamfe ]insa a filin fareti na Lafiya ya yi kira ga al’ummar jihar da su za~i shugabanni na }warai da za su kawo masu ci gaban rayuwa da kuma tattalin arziki a jihar.
[an takarar gwamnan ya yi kira ga al’ummar Jihar Nasarawa da su guji siyasar ku]i, don samun ci gaba da kuma }aruwar arziki, yana cewa, shugabanci daga Allah ne.
Ya yaba wa magoya bayansa saboda halin da ya kamata da suka nuna, tare da kiran su da su ci gaba da goyon bayansa don cimma burinsa.
Alhaji Aliyu Doma ya taya gwamnan jihar, Dokta Abdullahi Adamu murna saboda nasarara da aka samu wajen ba shi sarautar gargajiya a Idah ta Jihar Kogi da kuma Jihar Enugu, tare da al}awarin ci gaba da goyon bayansa bisa burinsa na rneman shugabancin }asar nan a shekara ta 2007.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban taron, Alhaji Halilu Bala Usman (Sarkin Fadan Nasarawa) ya yi kira ga jama’a da su za~i mutumin kirki, domin su samu ribar dimokura]iyya.
Har ila yau, ya yi kira gare su, da su yi amfani da }warewar ]an takarar neman gwamnan a fannin aikin gwamnati da kuma ~angaren mai zaman kansa, don samu ci gaba a jihar.
Wakilin mu ya ruwaito cewa, taron ya samu halartar ]imbin jama’a da masu yi masa fatan alheri.
Za A Mayar Da Ma’aikatan Da Suka Janye Daga Takara Bakin Aiki A Nasarawa
AN tabbatar wa ma’aikatan gwamnati da suka ajiye aiki don takarar za~en fitar da gwani na PDP da aka kamala kwananan zuwa majalisar dokokin jihar, kuma suka janye don son ran su ga wasu cewa za su sake komawa bakin aikin su.
Shugaban PDP a jihar, Alhaji Yusuf Ayitogo (Katukan Adudu) ne ya bayyana haka, a lokacin da yake kar~ar rahoto daga shugaban kwamitin sulhu da kuma tantancewa, }ar}ashin Furofasa Musa Bawa.
Shugaban PDP na jihar, Alhaji Yusuf Ayitogo ya ce, wanna shawarar da jam’iyyar ta zatar na sake mayar da ma’aikata da suke janye don kansu, an yi haka ne don }yale su su ci gaba da aikinsu, bayan da suka amince, ba za su kawo cikas ba a siyasar don wani buri na son zuciya.
Ya yaba wa irin wa]annan ma’aikatan gwamnati saboda shawarar da suka zatar na janyawa don barin wasu, musamman da gwamnati ta yi taro tare da su,akan hanyoyin da za a bi, don }ayyade adadin ‘yan takare zuwa majalisar dokokin jihar, a yayin za~en fitar da gwani.
Alhaji Yusuf Ayitogo ya yaba wa shugaban kwamitin, Furofasa Musa Bawa da wakilansa, saboda kyakkyawan aikin da suka yi, wanda ya sanya aka samu nasara wajen shirya za~en.
Tun da farko, shugaban kwamitin, Furofasa Musa Bawa ya ce, ‘yan takar 11 ne suka janye daga takarar, bayan tarururukan aka yi tare da su.
Ya yaba wa shugaban PDP na jihar saboda wannan dama da ya ba su, don su yi wa jama’a aiki, tare da bayyana cewa, a shirye suke su sake bayar gudumawar su don ganin jihar ta samu ci gaba.
Halin da ake ciki kuma, ]an takara daga maza~ar Lolo da Udage a za~en fitar da gwani da aka kammala [anladi Madaki ya yi kira a soke za~en fitar da gwani da aka yi a maza~arsa.
Ya ce, zai gabatar da wannan batu ga ofishin PDP na jihar, a bisa yun}urinsa na ganin an yi adalci a gare shi da kuma jama’arsa.
Da yake mayar martani bisa wannan batun, shugaban PDP a jihar, Alhaji Yusuf Ayitogo, ya ce, dukkan ‘yan takarar da suke da koke-koke suna da damar su gabatar da }ararakinsu a gaban kwamitin sauraroron }araraki da tuni aka fara don samun zaman lafiya.
Tuesday, November 28, 2006