Wani Yaro Ya Jagoranci Yi Wa Kawunsa Makaho Fashi
Daga Ahmad Musa, Kalaba.
RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Riba na tsare da wani matashi ]an shekara 19 mai suna Okechukwu Akani bisa tuhumarsa da laifin jagorantar ‘yan fashi da makami su yi wa kawunsa wanda makaho ne fashi a gidansa da ke Lamba 32 layin Ikot-Eyo da ke yankin Ikot a birnin Kalaba.
Jami’in hul]a da jama’a na rundunar Mista Jom Adama Okpene ne ya shaida wa jaridar Nasara haka a Kalaba. Kakakin ‘yan sandan ya ci gaba da cewa dubun yaron ta cika shi da ‘yan uwansa ~arayin ne bayan da aka }yan}yasa wa ‘yan sanda labarun aukuwar lamarin kuma samamen da suka kai ma~oyar ~arayin sai suka yi sa’ar cafke su.
Har wayau, Mista Adama Okpene ya tabbatar da cewa sun sace ku]in makahon Naira dubu 75.
Wakilinmu ya yi }o}arin jin ta bakin Okechukwu Akani game da yadda aka yi ya san inda ku]in suke, sai ya ce "Wani na cikin gidan ne ya gaya mini, shi ne na jagoranci abokaina bayan ya dawo daga tallar kanazir muka hai masa hari amma ba mu raunata shi ba bugu" da }ari yaron ya fada wa Nasara cewa, gigita shi kurum suka yi tun da makaho ne ba gani yake yi ba.
A wata sabuwa rundunar ‘yan sanda jihar ta dam}e wasu daliban Jami’ar Kalaba su biyar da ake zargin ‘yan }ungiyar asiri ne. An kama su ne a wani kurmi kusa da kogi a Atimbo lokacin da suke rantsar da sababbin ‘ya’yan }ungiyar. An same su da bindigogi da adduna yayin rantsar da sababbin shiga }ungiyar, in ji kakakin ‘yan sandan.
Tuesday, November 28, 2006