Za~en Wakillan Gundumomi Na PDP:
Na]i Aka Yi Ba Za~e Ba A Bauci -Yuguda
Daga Mu’azu Har]awa, Bauci.
BABBAN Daraktan kamfen ]an takarar gwamnan Jihar Bauci }ar}ashin jama’iyyar PDP, Alhaji Isa Yuguda, tsohon shugaban }aramar hukumar Gamawa Alhaji Lele Raga ya bayyana rashin gamsuwarsa game da irin rashin adalcin da aka yi musu a lokacin gudanar da za~en wakilan gudumomi da ya gabata.
Alhaji Lele Raga, ya ce, a ranar wannan za~e an ci mutuncinsu har sai da takai an kashe musu magoyan baya a garin Bunuu tare kuma da }ona musu gidan wani masoyi mai goyan bayan Malam Isa Yugudan, mai suna Malam Yukubu Wowo.
Ya ce, su a shirye suke a gudanar da harkokin siyasa lafiya cikin adalci, a ba wanda ya yi nasara nasararsa, amma sai ga shi gwamnatin Jihar Bauci ta shigo, tana neman wargaza al’amura wajen take ha}}in magoya bayansu, lamarin da ya bayyana cewa kashi 96 cikin 100 a ko’ina ba a gudanar da za~e ba, na]i kurum aka yi.
Ya ce, a dukkan wuraren da aka ce, za a yi za~en idan mutanensu suka bayyana a wuraren, sai su iske babu wani da ya zo daga ofishin jam’iyyar ta PDP, amma sai suka ji har an gama za~e sun tashi.
Alhaji Lele Raga ya ce, wannan kama-karya lamari ne mai ban tsoro da ba zai haifar da zaman lafiya a fagen siyasar Jihar Bauci ba, kuma ya ce, hakan zai iya wargaza jam’iyyar ta PDP.
Saboda haka ya nemi uwar jam’iyyar ta }asa da ta soke za~en, ta sake wani.
Lele Raga ya shawarci jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen ganin an bi doka dangane da fuskantar za~en 2007 lafiya. Ya ce, idan aka ci gaba da tozarta su, za su ri}a kare kansu. Ya ce, suna hamayya ta ci gaban ce ba ta cin zarafin wani ba.
Da yake amsa tambayoyin wakilinmu, kwamishinan ‘yan sanda Jihar Bauci, Tolman Adnan Gaya ya tabbatar da mutuwar mutum guda lokacin za~en tare da kama mutum hu]u a hannun doka.
Adnan Gaya, ya ce, rundunar ‘yan sanda ta sami }ararraki da yawa daga Toro da Yalwa da Tafawa Balewa da Bauci da suka shafi ma’amala da makamai da cin zarafi.
Ya ce, jam’iyyar PDP a Jihar Bauci ta rabu gida biyu, akwai magoya bayan gwamnatin Ahmadu Mu’azu da kuma na tsohon Minista, Malam Isa Yuguda, ya ce, wannan yana barazana ga har}o}in siyasa a jihar don haka ya shawarce su da su yi }o}arin daidaita tsakaninsu don a samu nasarar yin za~u~~uka masu zuwa.
Adnan Gaya ya ce, abin takaicin shi ne da su tsare mutane kan batun siyasa sai ka tarau yara ne matasa ‘yan shekaru 20 zuwa 25 ‘ya’yan talakawa su kuma manya kuma nasu yaran suna gida. Don haka ya shawarce su da su daina mayar da siyasa ko a mutu, ko a yi rai, don son zuciyar wa]ansu, }alilan ]in mutane.
Tuesday, November 28, 2006