Sa-In-Sa Tsakanin Gwamnatin Bauci Da Jam’iyyun Hamayya
Daga Mu’azu Har]awa, Bauci.
GAMAYYAR jama’iyyun hamayya a Jihar Bauci, sun nuna rashin yarda kan yadda gwamnatin jihar da majalisar dokokin jihar suka }ara wa’adin shugabannin }ananan hukumomi jihar ta }ir}iro dokar da ta mayar da su kantomomin ri}o.
Alhaji Shehu Barau Ningi, sakataren jam’iyyar ANPP na Jihar Bauci shi ne, ya bayyana haka a madadin sauran jam’iyyun siyasar wajen wani taron manema labaru da suka kira a cibiyar ‘yan jarida da ke Bauci.
Shehu Barau ya ce, abin takaici ne yin karan-tsaye ga tsarin mulki, domin }ara wa’adin, duk da cewa }a’idar da doka ta ]ibar musu ta wuce.
Ya ce, abin takaici ne, a ce, majalisar dokokin Jihar Bauci da umurnin Gwamna Ahmadu Mu’azu, ta shiga ]aki, ta bi umurnin doka ta saukar da shugabannin sannan kuma daga baya ta }ir}iro wata doka ta ba su ri}on }ananan hukumomin inda ya ce, hakan al’amarin ne da ya sa~a wa doka da tsarin mulki.Ya ce, a shirye suke su tafi kotu kan batun, don ganin an dakatar da wannan al’amari.
Ya }ara da cewa, su ma jam’iyyun adawa suna da ha}}i cikin na]in da za a yi, na ba su wakillai cikin shugabannin }ananan hukumomin da kansiloli.
Shehu Barau Ningi ya }ara da cewa babu wani abu na a zo a gani da gwamnati nan ta yi na farfa]o da masana’antu ko ingata ilimi, inda ya ce, duk kamfanoni sun mutu murus, har ma da wa]anda ta jibga ku]i don gyara su a lokacinta, inda ya yi misali da kamfanin nama da kamfanonin noma da na roba da ta yi.
Tuesday, November 28, 2006