Skip to main content.

 

Ina Zaune Da Sarakuna Lafiya - Inji Aliero


KWANAKIN baya Gwamna Muhammed Adamu Aliero na Jiher Kebbi ya ziyarci bu]e gasar Musaba}ar karatun Al}ur’ani ta }asa, a matsayinsa na babban ba}o. Don haka wakilinmu a Bauci Mu’Azu Har]awa ya samu tattaunawa da shi, ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ranka ya da]e, me za ka bayyanawa masu karatu game da tattaki da ka yi zuwa Jihar Bauci.

Da farko zan yaba game da irin ayyukan ci gaba na raya }asa da na ga Gwamna Ahmadu Adamu Mu’azu ya aiwatar a Jihar Bauci. Kuma ina yi wa jama’ar Bauci murna, saboda bai karya musu kara a ido ba.

Ko me ya sa ka bar jam’iyyar ANPP zuwa PDP duk da cewa ita ce ta fito da kai ka yi rawar gaban hantsi?

Ni, ko me a ke ciki, ni ne shugaban ANPP ko na bar ta ban barta ba, kuma ina goyon bayan ]an takararta na shugaban }asa sosai.

A lokacina ne aka fitar da Sarkin Gwandu, Alhaji Mustapha Jakolo daga Sarauta ko me ya kawo siyasa ta shiga sarauta hakan ya faru?

Na sha fa]i cikin taruka, duk wani abin da zai jawo rashin tsaro ko zaman lafiya ga Jihar Kebbi da }asa baki ]aya ba za mu amince da shi ba don mun fuskanci za a iya kaiwa ga rashin zaman lafiya ko rasa rayuka, don haka dole mu yi abin da zai haifar da bin doka da oda.

Kwamishinan watsa labaruna ma yana cikin wa]anda za su yi mini shaida wajen sasanta wannan batu, tun da shi sarki ne, mai babbar daraja, kuma abokan aikinsa sarakunan Jihar Kebbi duk muna zaune da su lafiya, babu wanda hakan ta rutsa da shi.

Sakamakon }aruwar rashin tabbas a fagen siyasar }asar nan yaya ka yi nazari za a iya magance matsalolin siyasa da suke faruwa a halin yanzu ?

A halin yanzu ana ci gaba da rijistar masu za~e tun daga shekarar 2003 ba a sake ba sai yanzu, amma kuma aikin na tafiyar hawainiya injinan ba su da kyau, ba a isar da su ga jihohi a wadace ba, kowane gwamna da kwamishinonin za~e duk suna kuka game da aikin na hukumar za~e mai zaman kanta, don haka dole a yi gyara.

Abu na biyu, shi ne a samar da tsaro a }asar nan, jami’an ‘yan sanda su tashi a tsaye su shirya, don tunkarar za~e na shekara ta 2007 bil ha}}i da gaskiya, don ganin an yi za~e cikin kwanciyar hankali da lumana.

Hanyar da kurum za mu gyara siyasa a }asar nan to dole shi ne a bi doka, mutane na han}oron samun mulki ta kowane irin hali ba tare da bin tsarin mulkin }asa ko dokokin da aka shimfi]a ba. Mutane suna cikin halin kwaso ‘yan bangar siyasa, don su ci zarafin abokan adawa, lamarin da yake mai muni ne a fagen siyasa. Dole doka ta yi aiki wajen ganin an sa kowa bin doka a lokacin za~e ko a bayan za~e. ‘Yan sanda su yi aiki na gaskiya, don samar da doka da oda. Amma idan ba an yi haka ba, to lallai za~en 2007 ni ina gani ba zai yiwu ba kwata-kwata.

A shekara ta 2007 ]an takarar shugaban }asa na jam’iyyarka ta ANPP Muhammadu Buhari ne, kuma a yanzu ga wasu gwamnoni a jam’iyyar sun fito, ya za ka iya bayyana mana hasashenka nan gaba?

Muhammadu Buhari shugaba ne da a ke darajawa a ANPP. Muna ba shi goyon baya, sosai, kuma yawan ‘yan takara ba shi ne wani abu ba kowa zai iya fitowa a fafata da shi ko dai ba gwamna yake ba zai sa ANPP a {asa ta sami tagomashi yana da damar da zai iya cin za~e, ba tare da wani ~ata lokaci ba, kuma yana da magoya baya.

Wane hasashe ka ke da shi kan za~u~~uka masu tahowa na shekara ta 2007.

Yanzu dai a halin da ake ciki }arancin kayan rijista shi ne muke ganin abu na farko da zai fara dagula al’amura, don haka muna kira ga hukumar za~e ta ]auki matakin gaggawa ta kawo kayan rijista ta raba su ga kowacce jiha. Idan ba haka ba, za~en ba zai yiwu ba.

Sannan akwai matsalar tsaro game da kashe-kashe da aka ta yi, yadda ake ganin idan da an yi aiki da ‘yan banga ba, to wasu ‘yan siyasa ba za su sami nasara ba, suna’barazana ga abokan hamayya, don haka lalle jami’an tsaro su ]auki matakin hana banga da ta’asa a cikin wannan siyasa, don a sami natsuwa da kwanciyar hankali, kowa ya fito ya yi za~e cikin walwala da kwanciyar hankali.

Su kuma talakawa su martab a ‘juna, su sani duk abin da mutum ya aikata lalle dole ya samu a }iyamarsa; na alheri ko na sharri. Haka su ma ‘yan siyasa su ji tsoron Allah, su tafiyar da harkokinsu cikin tsoron Allah da tausaya wa jama’a; da haka sai Allah ya tausaya mana, a yi komai lafiya a gama lafiya. Na gode.


Tuesday, November 28, 2006