Skip to main content.

 

Ba Lulu Ne Matsatar ‘NFA’ Ba - Owolabi


Daga Hamza Alhassan, Abuja

TSOHON ]an wasan }ungiyar }wallon }afa ta }asa ‘Green Eagles’ kuma tsohon watili a hukumar wasan }wallon }afa (NFA) Mista Felix Owolabi ya soki wa]anda suke kiran a cire shugaban hukumar ‘NFA’ Alhaji Sani Lulu. Owolabi ya ce ba wai yana goyon bayan Lulu ba ne amma gaskiyar magana ita ce matsalar }wallon Kafa a Nijeriya ba shugaban hukumar ‘NFA’ ba ne amma wa]anda suke kiran kansu masu gudanar da harkar }wallon }afa da kuma gwamnati wa]anan su ne matsalar harkar }wallon }afa a Nijeriya.

Mista Felix Owalabi ya ce ‘yana jin cewa wa]anda suke kiran kansu masu fa]a a ji a harkar }wallon }afa a Nijeriya su ne wa]anda kuma suka ka]a wa Sani Lulu }uri’a don zama shugaban hukumar ta ‘NFA’ za su mayar da ‘yan Nijeriya wawaye Idan yanzu suka ce shi Sani Lulu bai dace ya zama shugaban hukumar ta ‘NFA’ ba.

Owolabi wanda aka fi Sani da Owoblow ya zargi gwamnati kan yadda take }yale mutane su shugabanci tafiyar da harkar }wallon }afa ba tare da bayyana ci gaban da za su samar idan suka sami nasarar hawa kujeran ta ‘NFA’ ba.

Ya ce "ina ganin babu amfani kiraye-kirayen da wa]ansu suke yi don a cire Sani Lulu daga kan kiyerar ‘NFA’!


Tuesday, November 28, 2006