Skip to main content.

 

Bayan Ha]arin Mota: Na Yi Sa’a Har Yanzu Ina Raye-Westerhof


TSOHON mai’ hora da ‘yan wasan }ungiyar }wallon }afa ta }asa ‘Super Eagles’ Mista Clement Westerhof ya bayyana tsallake rijiy da baya da ya yi da cewa wani abin mamaki ne.

Westerhof wanda ya bayyana yadda wani ha]arin mota da ya rutsa da shi ya faru ya ce muna hanyarmu daga Abuja zuwa Ilorin ne a lokacin da ha]arin ya faru. "Motarmu tana tafiya sai kawai ta }wace ta shiga daji, mun yi sa’a babu itatuwa da duwatsu a inda motar ta fa]a da yanzu ana fa]in wani labari daban" in ji tsohon mai horar da ‘yan wasan da ya fi kowanne mai horar da wasan Nijeriya samun nasara.

A kowace magana da yake yi yana nuna godiyarsa ga Allah don yadda ya tsarar da su, shi da matarsa ‘yar }asar Afirka ta Kudu ya ce, muna murna kuma mun yi sa’a. Har yanzu Mista Westerhof yana kar~ar magani don buguwar da ya yi a wuyansa da kuma sassan jikinsa.


Tuesday, November 28, 2006