Skip to main content.

 

Katsinawa Na Shirin Botsare Wa PDP A Za~en 2007


Daga Salihu I. I. Makera, Kaduna

AL’UMMAR Jihar Katsina sun yi barazanar botsare wa jam’iyyar PDP a za~e mai zuwa muddin ta kuskura ta tilasta musu ]an takarar gwamnan da ba sa so, a za~en 2007.

Wata takardar bayan taro ]auke da sanya hannun uku daga cikin masu son jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar gwamnan jihar, da suka ha]a da shugaban majalisar wakilai Alhaji Aminu Bello Masari da Jakada Magaji Muhammad da kuma Alhaji Murtala Ibrahim Safana ce ta bayyana haka.

Taron wanda ya gudana }ar}ashin jagorancin wani jigo a jam’iyyar PDP Iro Abubakar [anmusa, {ungiyar Ma’abuta Neman ‘Yanci Da Ci Gaban Jihar Katsina ce, ta kirawo shi a Gidan Arewa da ke Kaduna ranar Lahadin makon jiya.

Takardar bayan taron ta ce, wajibi ne jam’iyyar PDP a jihar ta yi abin da ya ce, tare da ba magoya bayan jam’iyyar ‘yancin za~en ]an takarar da suke so muddim tana so jama’a su za~e ta a za~e mai zuwa.

Takardar ta ce, an yi mummunan mahangur~a wajen za~en wakilai masu za~en ‘yan takara domin a da}ile wa]ansu daga tsayawa takara tare da ba wani ]an takara mai uwa a gindin murhu damar rawar gaban hantsi.

Takardar ta ce, "Ba a gudanar da za~en wakilai masu za~en ‘yan takara ba a mafi yawan }ananan hukumomin jihar, maimakon haka an rubuta sunayen wa]anda ake so ne kawai lamarin da ke nuna shugabanni ba su girmama dimokura]iyya da kuma doka."

Takardar ta }ara da cewa, gidan gwamnatin Jihar Katsina ya koma sakatariyar ya}in neman za~e na ]an takarar da ke da uwa a murhu, yayin da shugabannin }ananan hukumomin jihar, suka zamo ko’odinetocin ya}in neman za~ensa.

Takardar ta ce, taron ya yi ittifa}i kan cewa duk wani yin}uri da za a yi don ]ora wa jama’ar jihar ]an takarar da ba shi suke so ba, zai ha]u da mummunan turjewa daga jama’ar jihar.

"Kuma duk rukunin masu son zuciya da ke tunanin za su mulki jihar a 2007, ta ko }a}a ha}arsu ba za ta tarar da ruwa ba, saboda al’ummar jihar sun ha]e domin }wato ‘yancinsu."

Domin cimma wannan manufa takardar ta ce, ]aukacin jam’iyyun da suka halarci taron na Kaduna da suka ha]a da ANPP da PDP da PRP da PSP da DPP sun yanke sawarar yin aiki kafa]a-da-kafa]a don tabbatar da adalci da ba wa jama’a ha}}insu a fagen siyasa, kuma idan har gwamnatin Katsina ta nuna ta fi son wani ]an takara, to za su fitar da ]an takara guda da ya dace don }alubatantar ]an takararta.

Wannan taro na Kaduna ya biyo bayan taron da ‘yan takarar uku suka fara yi ne a Katsina da malamai da shugabannin addini.

Wa]anda suka halarci taron na Kaduna sun ha]a da shugaban ANPP reshen Jihar Katsina Alhaji Yusha’u Armaya’u da na DPP Ibrahim Maidabino da wakilin na ‘AC’, Alhaji Kabiru Yahya da shugaban ‘PRP’ Alhaji Yusuf Abba da Alhaji Ahmed Abubakar Funtuwa na PSP da Alhaji Amadi Kurfi da Alhaji Halliru Abdullahi da Alhaji Iro Abubakar [anmusa, wakilai a kwamitin amintattun jam’iyyar PDP da malaman addini da kuma ‘yan siyasa da dama.

Sai dai a wani martani Gwamna Umaru Musa ‘Yar’aduwa ya musanta wannan zargi inda ya ce bai tsayar da wani ]an takara a hukumance ba.

Gwamnan wanda ke magana ta bakin kakakinsa Malam Nasiru Abdul ya ce, alhakin tsayar da ]an takara ya rataya a wuyan wakilan jam’iyya ne, ba wuyansa ba.

Gwamnan ya shaida wa Muryar Amurka a ranar Larabar da ta shige cewa, a matsayinsa na mutum shi ma yana da ‘yanci ya nuna sha’awa ga wani ]an takara, to ‘amma wannan ba ya yana nufin cewa shi kenan ya za~a wa mutanen jihar magajinsa ba.

Ya ce, wakilan jam’iyya ne suke dar yancin tsayar da wanda zai gaje shi, kuma ya ce, taron na Kaduna hayaniya ce kawai aka yi maimakon neman gyara.


Tuesday, November 28, 2006